Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fashewar tankar mai ya hallaka mutane 2 a kudancin Najeriya
2019-10-18 09:30:15        cri

A jiya Alhamis fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 2 a sanadiyyar fashewar tankar dakon mai wadda ta haddasa mummunar barna a ranar Laraba a jihar Anambra dake shiyyar kudancin kasar.

Sanarwar fadar shugaban kasar ta ce, an tabbatar da mutuwar wata mata da danta bayan da tankar man ta fadi, inda man ya dinga malala a kan titin Onitsha, babban birnin jihar ta Anambra mai yawan hada hadar jama'a,

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, ya yi matukar kaduwa bayan da ya kalli gawarwakin matar da danta, wadanda hadarin ya rutsa da su, a cewar sanarwar da aka fitar a Abuja.

Shugaban ya mika sakon jajantawa ga wadanda hadarin fashewar tankar man ya lalata gidajensu, da shaguna da sauran dukiyoyin jama'a.

Kafafen yada labaran yankin sun rawaito cewa, sama da gine gine 40 da wasu shaguna ne wutar ta kone.

Shugaba Buhari ya yi kiran gaggawa ga wadanda ke da ruwa da tsaki da su tabbatar da daukar matakan hana faruwar makamancin wannan mummunan hadari a titinan motar kasar.

Haka zalika shugaban na Najeriya ya umarci ma'aikatu da hukumomin da abin ya shafa, da kuma masu ruwa da tsaki da su gaggauta shawo kan wannan matsalar a duk fadin kasar, domin hana faruwar hakan a nan gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China