Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara aiki da sashen farko na hanyar dogo ta Nairobi-Malaba
2019-10-17 13:01:53        cri
A jiya Laraba, an fara aiki da sashen farko na Layin dogo na Nairobi-Malaba, wanda kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin gina ta.

A wajen bikin kaddamar da hanyar, shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewa, fara aiki da wannan hanyar zai samar da karin damammakin ci gaba ga yankunan Kenya da ma kasashen Uganda, Sudan ta kudu, da Burundi wadanda ke makwabtaka da ita, baya ga haka, hanyar zata kuma inganta matsayin kasar ta Kenya na mahadar zirga-zirga a shiyyar.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin dake Kenya, Wu Peng ya bayyana cewa, bunkasa hanyoyin layin dogo a kasar Kenya zai kara samar da alfanu ta fannonin zaman al'umma da ma tattalin arziki, kuma sannu a hankali za a iya gano karin nasarorin hadin gwiwar kasashen biyu ta fannoni daban daban. Har wa yau, jakadan ya ce, kaddamar da hanyar zai kara inganta hanyoyin dogo a gabashin Afirka, wanda zai taimaka ga dunkulewar yankin gaba daya, wanda kuma ke da matukar ma'ana ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma a Kenya da ma yankin gabashin Afirka baki daya.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China