![]() |
|
2019-10-16 10:55:42 cri |
Jack Ma ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Steve Forbes, shugaba, kuma babban editan kamfanin Forbes Media, yayin taron manyan jami'ai na bana da kamfanin Forbes ya shirya a Otel din Shangri-La na kasar Singapore.
Jack Ma ya ce manufarsa ita ce, mayar da 'yan kasuwar Afrika gwaraza, saboda 'yan kasuwa su ne jigon ci gaban al'umma, yana mai cewa, akwai karin abubuwan da za a iya yi don tallafawa mata 'yan kasuwa na Afrika.
A watan da ya gabata ne Jack Ma, ya sauka daga mukaminsa na shugaban kamfanin Alibaba.
Taken taron na bana shi ne "shawo kan Tangardar". Akan shirya irin taron ne a kowacce shekara, inda yake samun mahalarta sama da 400 daga fadin duniya da suka hada da shugabannin kamfanoni da kanana da hamshakan 'yan kasuwa da masu zuba jari da malamai, domin tattauna muhimman batutuwan dake ciwa duniya tuwo a kwarya da kuma kulla sabuwar dangantaka. Yayin taron an karrama Jack Ma da lambar yabo ta Malcolm S. Forbes, wadda ake ba kwarzon dan kasuwa. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China