Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta damu da hare-haren Turkiyya a arewacin Syria
2019-10-15 12:47:09        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya damu ainun da hare haren soji a arewa maso gabashin Syria, la'akari da yadda suke kara rutsawa da fararen hula, inda adadin wadanda suka rasa matsugunansu ya karu zuwa 160,000.

A cewar kakakinsa Stephane Dujarric, sakatare janar din na ci gaba da yin kira da a yi taka tsantsan, yana mai tunatar da cewa, dole ne duk wani matakin soji ya mutunta dokokin kasa da kasa, tare da ba da damar kai agaji.

Sakatare janar din ya bayyana damuwar cewa, rikicin zai iya haifar da wasu abubuwa, ciki har da sakin fursunonin kungiyar IS.

Stephane Dujarric, ya kara da cewa, ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD ya ce, daga cikin maza da mata da yara kimanin miliyan 3 dake arewa maso gabashin Syria, yanzu haka, miliyan 1.8 na bukatar agaji, ciki har da sama da 910,000 dake cikin tsananin bukata da kuma kusan 710,000 da suka rasa matsugunansu.

Yayin da ofishin ke ci gaba da tsara wata dabara ta daban, ma'aikatan agaji na MDD sun kuduri niyyar ci gaba da zama a yankin, lamarin da ya sanya MDD damuwa da tsaron lafiyarsu.

A bangaren siyasa kuma, Geir Pedersen, manzon musammam na MDD a Syria, ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Turai 28 jiya Litinin a Luxemberg, inda ya yi kira ga wadanda suke yaki a arewa maso gabashin Syria, su kaucewa duk wani mataki da zai musgunawa fareren hula da keta 'yancin kan kasar da kara rikita yanayin da ake riritawa da kuma illata kokarin da ake na farfado da tsarin siyasa a kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China