![]() |
|
2019-10-11 11:15:40 cri |
Arkebe Oqubay, minista, kana babban mashawarci ga firaministan kasar Habasha Abiy Ahmed Ali, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin bikin kaddamar da sabon littafinsa wanda aka gudanar a cibiyar masana tsara dabarun cigaba dake Rabat.
Da yake gabatar da littafinsa mai suna "Sin da Afrika da sauye-sauyen tattalin arziki" Oqubay ya ce, ya kamata kasashen Afrika su yi koyi daga muhimman nasarorin kasar Sin, kasar da a yanzu haka ita ce ke sahun gaba a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki.
Da yake tsokaci kan dangantakar dake tsakanin Afrika da Sin, Oqubay ya bukaci kasashen Afrika su yi kyakkyawan amfani da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika, wanda a cewarsa tana taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauye-sauye ga tsarin bunkasuwar masana'antun nahiyar Afrika. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China