Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU za ta bullo da shirin amfani da fasahar zamani wajen hana mutane barin gidajensu
2019-10-11 10:21:31        cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta sanar da bullo da wani sabon shiri wanda za'a dinga amfani da fasahar zamani wajen dakile matsalar tilastawa mutane kauracewa muhallansu da magance kalubalolin da suka shafi sauran ayyukan bada jin kan bil adama a fadin nahiyar Afrika.

Shirin, mai taken "Sabuwar fasahar dakile kalubalolin ayyukan jin kan bil adama," zai mayar da hankali ne wajen zabar fasahohin zamani biyar na Afrika don amfani da su wajen warware matsalolin tilastawa mutane kauracewa gidajensu, da kuma sauran batutuwan da suka shafi kabalubalen ayyukan jin kan bil adama wadanda dan adama ke haifar da su da wadanda ke faruwa daga min indallahi a nahiyar Afrika, wanda ya hada matsalolin rikice-rikice, fari, yunwa, ambaliyar ruwa, da barkewar cututuka da dai sauransu.

A cewar AU, manyan masu samar da fasahar kirkire-kirkire na Afrika biyar, wadanda za'a zaba karkashin sabon shirin, za'a ba su gajeriyar damar amfani da wasu dakunan gwaje-gwaje a Nairobi, babban birnin kasar Kenya a watan Nuwamban wannan shekara, inda za su samu tallafin kwararru don su gabatar da irin tunanin da suke da su zuwa mataki na gaba.

Tawagar da suka gabatar da tunanin mafi karbuwa, za su samu kyautar euro dubu 20 wanda za su yi amfani da su wajen bunkasa tunaninsu su mayar da shi wata fasahar kirkire-kirkire, ko wata fasahar aikin bada hidima mai amfani. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China