Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Iran ba za ta raya makaman nukiliya ba, in ji Khamenei
2019-10-10 14:26:00        cri
Jiya Laraba, jagoran kolin kasar Iran Grand Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ba da jawabi cewa, kasar Iran tana da karfin raya makaman nukiliya, amma ba za ta yi hakan ba.

Cikin dogon lokacin da ya gabata, batun nukiliyar kasar Iran ya janyo hankulan kasa da kasa. Kasar Amurka da wasu kawayenta suna ganin kasar Iran na kokarin raya makaman nukiliya. Amma kasar Iran ba ta amince da zarge-zargen ba, ta ce ba ta raya makaman nukiliyar ba, amma tana da ikon yin amfani da makamashin nukiliyar.

A watan Yuli na shekarar 2015, kasar Iran da kasashe shida dake shafar batun nukiliyar kasar Iran, wato Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus, sun kulla yarjejeniya kan batun nukiliyar kasar Iran. Bisa yarjejeniyar, kasar Iran ta amince da takaita shirye-shiryen nukiliya na kasarta, kana gamayyar kasa da kasa sun soke takunkumin da suka sanya mata.

A watan Mayun shekarar 2018, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da janye jiki daga wannan yarjejeniya, sa'an nan, ya fara kakabawa kasar Iran sabbin takunkumai. Sa'an nan, a shekarar bana, kasar Iran ta dakatar da wasu sharrudan yarjejeniyar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China