Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta samar da kayayyakin aiki da kwararrun likitoci domin maganin cutar sankara a Sudan ta Kudu
2019-10-09 11:15:07        cri
Babban asibitin koyarwa na kasar Sudan ta Kudu, ya bayyana a jiya cewa, ya karbi kayayyakin aiki daga kasar Sin, wadanda za su taimaka wajen kulawa da masu cutar sankara, yayin da adadin mace-macen da cutar ke haifarwa ke karuwa saboda rashin magani da kayayyakin aiki.

Daraktan asibitin Maker Isaac, ya ce sun karbi sabbin kayayyakin aiki na maganin cutar sankara daga kasar Sin. kana nan bada dadewa ba, kwararru za su zo daga kasar, domin bude cibiyar binciken cutar, yana mai cewa ba sa son jama'arsu su mutu saboda cutar sankara da za a iya maganinta.

Ya ce kwararrun na kasar Sin ba su isa kasar ba tukuna, sai bayan an kammala shirya kayayyakin aikin a cibiyar binciken cutar. Yana mai cewa ba ga mutanen Juba kadai cibiyar za ta yi aiki ba, har ma da sauran jihohin kasar.

Ya kara da cewa, za a horar da wasu likitocin kasar ta Sudan ta Kudu kan yadda za su yi amfani da kayayyakin. Inda ya kara da cewa, za a horar da karin likitoci daga jihohin kasar daban daban a matsayin kwararru kan magance cutar sankara, domin rage kudin da ake kashewa na tura marasa lafiya kasashen waje. Daraktan ya ce har yanzu ba su da magungunan kulawa da cutar sankara a asibitin.

Kasar Sin na tallafawa wajen fadadawa da sake fasalin asibitin koyarwa na Juba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China