Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta kai samame maboyar 'yan kungiyar masu satar mutane
2019-09-26 11:05:28        cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta tabbatar da cewa wasu mutane 2 da ake zargin masu satar mutane ne sun mutu, biyo bayan samame da jami'an rundunar suka kai sansanoninsu a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an yi musayar wuta yayin da masu satar mutanen suka mayar da martani dangane da samamen, wanda aka kai bisa samun sahihan bayanan sirri.

Sai dai, kakakin 'yan sandan jihar Kamal Abubakar, ya ce 'yan sandan sun ci karfinsu, inda suka kuma lalata sansanin.

A cewarsa, wasu 'yan kungiyar da ba a san adadinsu ba, sun tsere da raunukan harbi.

Ya kara da cewa, an kuma gano albarusai da Babura a sansanin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China