Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rufe kan iyakokin Najeriya zai illata tattalin arziki, in ji wani masani
2019-09-25 19:34:08        cri
Tsohon darakta a babban bankin Najeriya Titus Okunrounmu, ya ce matakin rufe kan iyakokin kasar da wasu kasashe makwaftanta da gwamnatin Najeriya ta dauka, na iya haifar da matsi ga tattalin arziki ga kasar. Mr. Okunrounmu ya bayyana hakan ne, yayin wata zantawa da manema labarai a garin Ota dake jihar Ogun a kudancin kasar.

Okunrounmu, ya ce rufe kan iyakokin na iya iya zama kalubale, duba da cewa Najeriyar na shigo da tarin kayayyaki ne daga kasashen waje, kuma mai yiwuwa ne, masu fasakwauri su bullo da wasu dabarun shigar da kaya cikin kasar ta barauniyar hanya, wanda hakan ba zai haifarwa kasar da mai ido ba, ta fuskar haraji da Najeriyar ke samu daga shigar da kaya.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin kasar, da ta dauki wasu muhimman matakai, na bunkasa tattalin arziki, ta hanyar duba na tsanaki ga hanyoyin warware wannan kalubale.

A watan Agustan da ya gabata ne dai mahukuntan kasar, suka bayyana matakin rufe kan iyakokin Najeriyar da wasu kasashe makwaftanta, a wani mataki na dakile ayyukan 'yan sumoga. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China