Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin taya murnar cika shekaru 70 na kafuwar sabuwar kasar Sin a kasar Zimbabwe
2019-09-22 16:23:39        cri
An yi wani bikin nuna fasahohin al'adu a birnin Harare, hedkwatar kasar Zimbabwe, a daren jiya Asabar, musamman domin taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar Jama'ar kasar Sin, inda mutane fiye da dari daya suka kalli bikin, ciki har da jami'an gwamnatin kasar, da jakadun kasashe daban daban dake Harare, da ma jama'ar kasar ta Zimbabwe.

Yayin bikin, masu fasahohin al'adu na kasashen Zimbabwe da Sin, sun nuna fasahohin taka rawa, da rera wakoki, da wasan kundumbala, da bikin nuna tufafin gayu, inda suka nuna zumuncin dake tsakanin kasashen 2, gami da ci gaban da aka samu a kokarin zurfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin 2.

Oppah Muchinguri-Kashiri, shugabar jam'iyyar Zanu-PF, kuma Ministar tsaron kasar Zimbabwe, ta yi jawabi a wajen bikin, inda ta ce ci gaban da kasar Sin ta samu ya zama fasahohi masu amfani ga sauran kasashe masu tasowa, wanda ke karfafa gwiwar kasar Zimbabwe a kokarinta na neman zama kasa mai matsakaicin kudin shiga.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China