Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun AU da wasu kasashen Afirka sun ziyarci Xinjiang
2019-09-17 20:13:41        cri

Jakadan kungiyar tarayyar Afirka AU dake wakilci a kasar Sin da uwargidansa, da wasu jakadu daga kasashen Afirka 16, wato Burundi, da Uganda, da Lesotho, da Afirka ta kudu, da Burkina faso da Kongo(Brazzaville). Sauran sun hada da na Mozambick, da Jibouti, da Sudan da Zimbabwe, sun ziyarci biranen Urumqi da Turpan na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta kasar Sin, tsakanin ranekun 9 zuwa 12 ga wata, bisa gayyatar da gwamnatin jama'ar jihar ta yi musu, domin yin rangadin aiki a unguwannin biranen, da cibiyar horas da kwarewar sana'o'i, da masallaci da kuma kamfanoni daban daban.

Yayin ziyarar ta su, sun yaba da sakamakon da jihar Xinjiang ta samu a fannonin ingiza ci gaban zaman jituwa, da kiyaye 'yancin bin addini, da yada al'adun gargajiyar kananan kabilu, da yaki da ta'addanci, kana sun bayyana cewa, ya dace a kara fahimtar ainihin yanayin da jihar Xinjiang ke ciki, ta hanyar kallon hakikanin abubuwa da idonsu. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China