Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane miliyan 3.9 na bukatar taimakon jin-kai a Mali
2019-09-14 17:04:45        cri
Stephane Dujarric, kakakin sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana jiya Jumma'a cewa, halin jin-kai na ci gaba da tabarbarewa a Mali, inda kasar ke da mutane sama da miliyan 3.8 dake bukatar taimakon jin-kai, duba da tashe-tashen hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa tsakanin al'ummomi daban-daban.

Stephane Dujarric, ya ce, yawan mutanen da suke bukatar taimakon jin-kai ya karu da kaso 22 tun daga farkon shekarar da muke ciki, kana kuma kaso 20 na jama'ar kasar Mali na rayuwa bisa tallafin kasa da kasa. Ya ce zuwa karshen watan Yuli, adadin mutanen da suka rasa matsugunansu a Mali ya tasam ma dubu 170.

Dujarric ya ce, har yanzu akwai mutane sama da dubu dari biyar a Mali wadanda ke rayuwa cikin matsanancin hali na rashin isasshen abinci.

Tun daga watan Maris din shekarar 2012 zuwa yanzu, yanayin siyasa da tsaro gami da fadace-fadace tsakanin kabilu a Jamhuriyar Mali na dada ta'azzara.

Bisa alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a watan Fabrairun bana, yawan sojojin majalisar na wanzar da zaman lafiya da suka rasa rayukansu a Mali a shekara ta 2018 ya fi yawan sojojin majalisar da suka mutu a sauran kasashe.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China