Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsaurara matakan kare hakkin mallakar fasaha da kasar Sin ta yi ya ja hankalin karin baki masu neman izinin mallakar fasaha
2019-09-14 16:00:20        cri
Hukumar kula da hakkin mallakar fasaha ta Kasar Sin, ta ce la'akari da kara tsaurara matakan kare hakkin mallakar fasaha bisa doka da kasar ta yi, baki masu neman izinin mallakar fasaha a kasar na karuwa.

A cewar mataimakin shugaban hukumar Gan Shaoning, daga watan Junairu zuwa Yulin bana, baki 92,000 ne suka nemi izinin mallakar fasaha a kasar Sin, adadin da ya karu da kaso 8.3, kuma wasu 149,000 na neman rejistar tambarinsu, wanda ya karu da kaso 13.1 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Da yake ganawa da wasu gungun 'yan jarida na kasashen waje, Gan Shaoning, ya alakanta karuwar alkaluman da aiwatar da jerin matakan karfafa kare hakkin mallakar fasaha a kasar, ciki har da gyara dokoki da gaggauta tsarin kare hakkin mallakar fasaha da kuma hukunta wadanda suka saba dokoki.(Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China