Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An rantsar da ministocin gwamnatin rikon kwarya a Sudan
2019-09-09 09:52:30        cri

Shugaban majalissar kolin kasar Sudan Abdel-Fattah Al-Burhan, ya jagoranci rantsar da sabuwar majalissar zartaswar kasar, yayin bikin da ya gudana a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar.

Jimillar ministoci 18 ne dai suka sha rantsuwar kama aiki a gaban Mr. Al-Burhan, da firaministan kasar Abdalla Hamdok, yayin da ake dakon nadin karin ministoci 2, wato na ma'aikatar samar da ababen more rayuwa da sufuri, da kuma na ma'aikatar kiwon dabbobi da kiwon kifi.

Jim kadan bayan bikin rantsuwar, mambobin majalissar sun gudanar da wani taron hadin gwiwa.

A ranar 5 ga watan Satumba ne dai, Hamdok ya sanar da kafuwar majalissar rikon kwaryar kasar, bisa tanadin kundin tsarin mulki, majalissa ta farko da za ta jagoranci kasar tun bayan kawar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

Kaza lika a ranar Lahadi, ministan ma'aikatar kudin kasar ta Sudan Ibrahim Elbadawi, ya sanar da shirin inganta tattalin arzikin kasar cikin kwanaki 200, shirin da a karkashin sa, za a aiwatar da muhimman matakan magance manyan kalubalen tattalin arziki dake addabar kasar.

Bayan ya yi rantsuwar kama aiki, Elbadawi ya shaidawa manema labarai cewa, sassa 5 da za a baiwa muhimmanci sun hada da inganta tattalin arzikin kasar bisa manyan tare-tsare, da yiwa tsarin kasafin kudin kasar garanbawul, da daidaita farashin hajoji, da kawar da tsadar rayuwa, da magance matsalolin matasa, da sauya akalar ci gaba a yankuna masu fama da tashe tashen hankula, daga tsarin dogaro da tallafi zuwa na wanzar da ci gaba mai dorewa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China