2019-08-29 20:29:16 cri |
Yau a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, kasar Sin tana mayar da martani kan takaddamar cinikayyar da Amurka ta tayar, kana tana adawa da tsanantar takaddamar, don haka tana son daidaita matsalar a hankali ta hanyar yin tattaunawa. Don haka, muddin ana bukatar magance tsanantar takaddamar a halin yanzu, ya dace a tattauna yadda za a soke matakin kara sanya haraji kan kayayyakin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan 550.(Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China