Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin tana sa ran kasashen Afirka su hada kai da kasashe daban daban
2019-08-29 19:09:37        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a wurin taron ganawa da manema labaran da aka saba shiryawa a yau cewa, kasar Sin tana sa ran taron kasa da kasa game da raya kasashen Afirka da ake gudanarwa a birnin Tokyo na kasar Japan zai ba da gudummawa kan ci gaban kasashen dake nahiyar Afirka.

Wasu kafofin watsa labarai na kasar Japan sun gabatar da rahotanni cewa, Japan ba ta sanar da adadin shugabannin kasashen Afirka wadanda suke halartar taron ba, kila ne tana tunanin ko kasar Sin za ta matsawa kasashen Afirka da suka halarci taron lamba.

Kan wannan, Geng Shuang ya jaddada cewa, har kullum kasarsa tana son ganin kasashen Afirka su gudanar da hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, abu mafi muhimmanci shi ne, wasu shugabannin kasashen Afirka sun taba bayyana cewa, kasashen Afirka ba su taba gamuwa da matsalar dammammakin shiga taron kasashen duniya ba, a don haka kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su cika alkawarinsu na samar da karin tallafi ga kasashen Afirka ta hanyar daukar hakikanan matakai, kana kasar Sin tana ganin cewa, ya dace kasashe duniya su kara mai da hankali kan ra'ayoyin kasashen Afirka, ta yadda za su dauki matakan da suka dace domin raya ci gaban Afirka yadda ya kamata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China