Kasar Sin ta sanar da gina wasu sabbin yankunan cinikayya na gwaji guda 6
2019-08-26 15:30:19 cri
A yau ne majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar da taswira game da gina wasu sabbin yankunan cinikayya na gwaji guda 6, a kokarin zurfafa gyare-gyare da bude kofa a sabon zamani.
Za a gina sabbin yankunan ne a lardunan Shandong da Jiangsu da Guangxi da Hebei da Yunnan da kuma Heilongjiang. (Fa'iza Mustapha)