Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin za ta goyi bayan a mayar da Shenzhen yankin gwaji mai halayyar gurguzu ta musamman
2019-08-20 11:51:28        cri

A ranar 18 ga watan nan, a cikin wata takardar bayani da gwamnatin kasar Sin ta fitar, an nuna cewa, za a gina birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, ta yadda zai zama yankin gwaji na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin mai matukar kayatarwa. Takardar bayani ta nuna cewa, gina wannan yanki zai taimaka wajen kara aiwatar da manufofin zurfafa gyare gyare, da kara bude kofa ga waje daga dukkanin fannoni. Aikin zai kuma tallafa wajen cimma nasarar aiwatar da manufar bunkasa yankin Guangdong zuwa Hong Kong zuwa Macao, tare da alamta cimma burin kasar Sin na zama kasa wadda ke farfadowa.

Birnin Shenzhen wanda ke kudancin lardin Guangdong na kasar Sin, yankin tattalin arziki na musamman na farko da kasar Sin ta kafa. A kan kira shi "wanda yake kan gaba" wajen kaddamar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofar kasar Sin ga ketare. A cikin shekaru 40 da suka gabata, birnin Shenzhen, wato wani karamin kauyen da ke makwabtaka da yankin Hongkong, ya zama daya daga cikin muhiman birane a duk duniya, sakamakon cin gajiyar kaddamar da manufofin yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare a kasar Sin. Yanzu, a bayyane take cewa a cikin wata takardar bayani da kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar, an nuna cewa, za a gina birnin Shenzhen dake kudancin kasar Sin, ta yadda zai zama yankin gwaji na gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin mai matukar kayatarwa. Shehun malami Li Guoping na cibiyar nazarin ilmin gudanar da harkokin biranen kasar Sin ta jami'ar Peking, yana ganin cewa, wannan ya alamta cewa, birnin Shenzhen zai sake zama a sahun gaba, wajen yin gwajin sabbin manufofin yin gyare-gyare da bude kofa da kasar Sin za ta aiwata a nan gaba.

"Birnin Shenzhen, wuri ne da aka riga sauran wurare kaddamar da manufofin yin gyare-gyare, da bude kofa ga ketare, da kuma bunkasa gurguzu mai halayyar musamman a kasar Sin, kana ya fi sauran wurare samun nasarori mafi yawa a kasar. A lokacin da ake tattauna maganar yin gyare-gyare da bude kofa ga ketare a kasar Sin, tabbas ne a tabo birnin Shenzhen. Yanzu, a lokacin da ake kokarin cimma burin gina gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin mai matukar kayatarwa, ko birnin Shenzhen zai sake samar da wasu abubuwan misalin koyo ga sauran wurare? A gani na, shi ne muhimmin dalilin da ya sa aka sanya birnin Shenzhen ya zama yankin gwaji."

A cikin wannan takardar bayani, birnin Shenzhen zai zama "inda za a samu ingancin ci gaba", da "birni mai kayatarwa", "inda al'ummu za su ji dadin zama a ciki", da kuma "birni wanda ke kan sahun gaba wajen neman ci gaba mai dorewa". Sannan an nemi a raya tattalin arzikin zamani da kuma kafa tsarin birnin na bincike da bunkasuwa, da nagartar masana'antu, da fadadar kirkire kirkirensa, tare da kyautatar hidimomin al'umma, da ma kyakkyawan yanayin muhallin halittun birnin, duka za su zamo a sahun gaba a duniya. Mr. Fu Zhengping wanda ke nazarin harkokin raya yankunan Guangdong da Hongkong da Macao a jami'ar Sun Yat-sen, yana mai cewa, "A cikin takardar, ba kawai an jaddada bunkasa tattalin arziki ba, yanzu ma an nemi a yi kokarin neman ci gaba daga dukkan fannoni, wato a lokacin da ake bunkasa tattalin arziki, dole ne a samu ci gaba a fannonin zaman al'umma, da harkokin siyasa, da na dimokuradiyya da na shari'a, da kare muhallin halittu da dai sauransu a birnin Shenzhen."

Takardar bayani ta nuna cewa, nan da shekarar 2025, Shenzhen zai zama daya daga manyan birane a duniya a fannin bunkasar tattalin arziki da ingancin ci gaba. Kaza lika tsarin birnin na bincike da bunkasuwa, da nagartar masana'antu, da fadadar kirkire kirkiren sa, tare da kyautatar hidimomin al'umma, da ma kyakkyawan yanayin muhallin halittun birnin, duka za su zamo a sahun gaba a duniya. Sannan, nan da shekarar 2035, birnin zai zamo sahun gaba a fannin karfin takarar tattalin arziki, da kirkiro sabbin fasahohin zamani, da sabbin hanyoyin neman ci gaba a duk fadin duniya. Bugu da kari, ya zuwa karshen karnin da muke ciki yanzu, birnin Shenzhen zai kasance kamar birni mafi shahara kuma abin koyi ga sauran biranen duniya, a fannonin samun karfin takara da kirkiro sabbin abubuwan zamani.

Mr. Song Ding, shugaban cibiyar nazarin harkokin yawon shakatawa ta kasar Sin yana mai cewa, "Yanzu, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga ketare, inda kasar take da wani nauyi a wuyanta, na ba da shugabancin ci gaban duk duniya a nan gaba. Sabo da haka, dole ne yanzu ta kafa wani yankin gwaji, domin kokarin sauke wannan nauyin dake bisa wuyanta a nan gaba. Sakamakon haka, wannan gwaji zai sha bamban sosai da raya wani yankin musamman na tattalin arziki kawai."

A cikin wannan takarda, gwamnatin kasar Sin tana kuma fatan za a hanzarta kafa wani sabon yanayin zurfafa yin gyare-gyare da bude kofa a birnin Shenzhen, ta yadda za a iya taimakawa bunkasa yankin dake kunshe da lardin Guangdong da yankunan Hongkong da Macao. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China