Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya aikawa ma'aikatan lafiya sakon gaisuwa
2019-08-19 21:03:30        cri

A yau ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya aikawa ma'aikatan lafiyar kasar gaisuwa da fatan alheri, yayin da kasar ke bikin ranar ma'aikatan lafiya karo na biyu.

Li ya umarci sassan da abin ya shafa, da su gudanar gyare-gyare a bangaren lafiya, da inganta tsarin biya da jin dadi da ma makomar ma'aikatan lafiya, da kyautata alaka tsakanin likitoci da marasa lafiya, kana su kara martaba ma'aikatan lafiyan.

Ya kuma yi kira ga ma'aikatan lafiyan, da su sadaukar da kansu wajen ceton rayuka, da inganta kwarewarsu, kare mutunci, su kuma nema hanyoyin magance manyan cututtuka kamar sankara.

Kasar Sin dai ta ware ranar 19 ga watan Agusta, a matsayin ranar ma'aikatan lafiya, tare da yin kira ga daukacin al'umma da su rika mutunta ma'aikatan lafiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China