Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kara bude kofa a bangaren hada-hadar hannayen jari ya karawa masu zuba jari na waje kwarin gwiwa kan kasar Sin
2019-08-18 16:06:51        cri

Kara fadada bude kofa a bangaren hada-hadar hannayen jari da kasar Sin ta yi, ya inganta yakinin masu zuba jari na ketare, wadanda suke kara sha'awar shiga kasuwannin kasar.

Shugaban sashen hada-hadar hannayen jari na kamfanin J.P Morgan mai hidimar hada-hadar kudi da hannayen jari, Houston Huang, ya ce suna da yakinin kan ci gabansu a kasar Sin.

Kamfanin na Amurka, na hada hannu da bangaren masu ruwa da tsaki da masu tafiyar da harkokin zuba jari na kasar Sin, domin ingiza kafa sabon kamfanonin hada-hadar hannayen jari a kasar Sin.

Sabon kamfanin mai suna J.P Morgan (China) Company LTD, ya zo ne a daidai lokacin da kasar Sin ke tsaka da kokarin kara bude kofar tattalin arzikinta, inda ta ba kamfanonin kasashen waje ikon mallakar kaso 51 na jarin kamfani daga kaso 49.

Sabon kamfanin zai ba J.P Morgan damar karfafawa da kara amfana daga kasuwar kasar Sin. (Fa'iza Msuatpha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China