Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudin shiga da ake iya kashewa na Sinawa ya ninka sau 60 a shekaru 70 da suka wuce
2019-08-11 16:22:21        cri
Albarkacin yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru 70 da suka wuce, kudin shiga da ake iya kashewa na jama'ar kasar ya ninka har sau 60, a cewar wani rahoton da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar.

An ce lokacin da aka kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, kudin shigar kowane mutum a duk shekara shi ne Yuan 49.7, bisa wani matsakaicin matsayi, yayin da wannan adadi ya kai Yuan 28,200, kwatankwacin dala 4030, a shekarar 2018. Idan aka yi la'akari da batun hauhawar farashin kaya, da tasirinsa, a jimlace adadin ya ninka har fiye da sau 59.

Yadda aka samu karin kudin shiga ya taimakawa samun karuwar kudin da ake kashewa a kasuwannin kasar. Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, kudin da kowane Basine ya kashe a duk shekara ya karu daga Yuan 88.2 na shekarar 1956 zuwa Yuan 19,853 na shekarar 2018, adadin da ya ninka har sau 28.5. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China