Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manufar "Tsugunar da masu fama da talauci a wuraren da suka dace" ta kyautata rayuwar iyalin Guan Ailing
2019-08-07 19:58:32        cri

 


Gidan Guan Ailing yana kusa da kamfanin da take aiki, tafiyar mintoci kimanin biyar ne kawai da kafa daga gidanta zuwa kamfanin. A ko wace rana da safe, bayan 'ya'yanta biyu sun tafi makaranta, sai ta taka da kafa zuwa kamfanin don ta soma aiki, ya zuwa tsakiyar rana kuma, ta ci abinci kyauta a kamfanin, bayan ta kammala aiki a ranar, sai ta koma gida don ta dafawa iyalanta abincin dare. A cewar Guan Ailing, babu wani nisa tsakanin gidanta da kamfanin da take aiki, kuma ba ta taba tsamanin cewa, za ta yi irin wannan rayuwar da take yi a yanzu ba.

Kafin shekarar 2017, iyalin Guan Ailing yana zama ne a wani yanki mai tsauni dake da nisan kilimita 15. Gidansu dakuna guda biyu da aka gina da tabo, babu ruwan famfo, kuma babu tsarin sufurin. Duk iyalan sun dogaro ne a kan mijinta, wanda ke aikin cin rani a waje. Guan Ailing ta gaya wa wakilinmu cewa, a 'yan shekarun da suka wuce, ta gamu da iftila'in kuna, lamarin da ya sa dole ta zauna a gida, mijinta yana aiki da kuma kula da ita, gaskiya sun sha wahalhalu sosai. Guan Ailing ta ce,

"Miji na ya fita waje neman aiki, shi kadai ne ya ke kokarin nema mana kudin shiga, ni kuma na kula da yara a gida. Mun sha wahala sosai a cikin wadancan shekaru, na ji rauni sakamakon kunar gas na ruwa, daga kai na har zuwa kafa ta ya kone, bana iya aiki sai kwanciya. Bana komai a wadannan shekaru biyar, a shekarar da ta wuce ne, na soma yin aiki a nan."

 

Yanzu iyalin Guan Ailing yana jin dadi ne sakamakon manufar "tsugunar da matalauta a wuraren da suka dace". Bisa manufar, a shekarar 2017, iyalin Guan Ailing sun kaura daga yanki mai tsauni zuwa al'ummar De Fu Yuan da yake zama a yanzu. Bisa ma'aunin da aka tsara, wato duk wani mai fama da talauci zai samu filin da ya kai muraba'in mita 25, an raba wa iyalin Guan Ailing mai mutane hudu wani gida mai fadin muraba'in mita 100.

Akwai al'ummomi kimanin 2600 dake zama a al'ummar De Fu Yuan, kamar iyalin Guan Ailing, dukkansu sun kaura zuwa nan ne daga yankuna masu tsauni dake fama da talauci. Shugaban garin Deting mista Guo Liwei ya gaya wa wakilinmu cewa, mazauna wurin sun fito ne daga iyalai masu fama da talauci na kauyuka 14 dake kusa da al'ummar, kuma dukkansu sun samu gidajen ne kyauta. Mista Guo ya ce,

"Tun daga shekarar 2016, mazauna al'ummar sun ci gajiyar hadaddiyar manufar da aka tsara, ko wane mutum zai iya samun muraba'in mita 25, kuma kyauta. Ban da wannan kuma, dukkan manyan kayayyakin more rayuwa gwamnati ce ta samar."

Mista Guo ya kara bayyana cewa, an soma gina al'ummar De Fu Yuan mai muraba'in kilomita 0.1 ne a shekarar 2015, inda aka zuba jarin da ya kai RMB miliyan 170, kwatankwacin dala miliyan 25. Akwai dakunan kwana guda 17, wadanda ke iya daukar iyalai guda 700 da ya kunshi mutane 2600. Dukkan manyan kayayyakin more rayuwa, ciki har da cibiyar saukaka rayuwar jama'a, cibiyar ayyukan al'udu, gidan renon yara, makarantar firamare da kuma cibiyar jinya da dai sauransu sun riga sun soma aiki.

Bisa babbar manufar daukar takamaiman matakai na yaki da talauci da gwamnatin kasar Sin ta tsara, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, an gudanar da wani babban aikin bincike a duk fadin kasar, sakamakon haka, aka samu hakikanan bayanai game da wuraren da masu fama da talauci suke zama, da dalilan da suka haddasa talauci, da kuma bukatun jama'a na kawar da talauci da dai sauransu. Ta hanyar bincike da aka yi, an gano cewa, akwai mutane kimanin miliyan 10 dake fama da talauci da har yanzu ke zama a wurare masu muhallin halittu. Don haka, gwamnatin kasar Sin ta mai da manufar "Tsugunar da masu fama da talauci a wuraren da suka dace" a matsayin daya daga cikin ayyukan ta na yaki da talauci, ta kuma tsaida kudurin tsara shekaru biyar don tsugunar da wadannan mutane masu fama da talauci a wuraren da suka dace kafin shekarar 2020, idan har suka kubuta daga wannan hali mai tsanani, da samar musu da kayayyakin rayuwa masu kyau, hakan zai taimake su wajen kara samun aikin yi, ta yadda za a cimma burin kawar da talauci yadda ya kamata.

Garin Deting na da girman muraba'in kilomita 321, yana cikin kungurumin tsauni, ana iya cewa, yana cikin wani mummunan yanayi, babu wurare masu yawa da jama'a za su zauna, kana gidajen mazauna suna da nisa da juna. Idan ana son kyautata yanayin zaman rayuwar mazauna wurin, to sai dai a kaurar da su daga wurin.

Shugaban garin mista Guo ya gabatar da cewa, ya zuwa yanzu yawan iyalai masu fama da talauci da suka yi rajista a wurin ya kai sama da 2500, kimanin mutane 9241. A cikin 'yan shekarun nan, an kafa al'ummomi guda takwas a wannan garin, wadanda suka kunshi iyalai kusan 1400 kimanin mutane sama da 5000.

Ko gwamnatin kasar Sin ta tilas ta wa wadannan mutane masu fama da talauci kaura zuwa wuraren da suka dace?, a'a ba haka ba ne, ana gudanar da wannan aiki ne bisa son ransu. Mista Guo ya gayawa wakilinmu cewa, ana gudanar da wannan manufa kan iyalai dake warware daban-daban, da wadanda ke zama su kadai. Ya ce,

"Da farko dai, ana gudanar da wannan aiki ne bisa son ran jama'a, na biyu, ga iyalai dake zama su kadai da tsofaffin da suka rasa iyalansu, to za a gargade su da su kaura, saboda yanayin da suke ciki bai dace da zaman rayuwarsu ba, kana ba za su iya ciyar da kansu a wurin ba."

Al'ummar De Fuyuan, tana daya daga cikin yankunan da aka tsugunar da mutane guda takwas na garin Deting. Aikin kaurar da matalauta hanya ce da gwamnati ta dauka, kawar da talauci yana daga cikin burin gwamnati. Domin kwantar da hankulan wadannan masu fama da talauci wajen kaura zuwa sabbin wurare, da kuma wadatar da su da kyautata zaman rayuwarsu, gwamnatin wurin ta dauki matakai iri daban daban don taimaka musu wajen kawar da talauci. Mista Guo ya ce,

"Da farko, mun yi amfani da fifikon al'ummar a fannin yankin musamman da take ciki, wato tana kusa da Tian Chi Shan, sharararren wurin shan iska na wurin, don inganta rayuwar iyalai 131 dake wurin wajen tafiyar da harkokin masaukan baki, hakan ya taimaka wajen raya sana'ar yawon shakatawa sosai. Na biyu, mun shigo da kamfanoni, don samar da guraban ayyukan yi ga wasu iyalai guda 57. Na uku, mun guraban ayyukan yi na jin kai a cikin al'ummar, ta yadda mazauna masu fama da talauci guda 14 suka samu aikin yi a fannin jin kai. Ban da wannan kuma, mun kafa wata tashar samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin hasken rana,wanda zai samarwa garinmu wutar lantarkin da ta kai kilowatts 1890, hakan ya taimaka wajen kara kudin shiga na iyalai kusan 500 dake garin. Kana mun kafa hukumomin hadin kai masu fasaha guda 25, don raya wasu sana'o'i na musamman, ciki har da maganin gargajiya na kasar Sin. Wadannan matakan da muka dauka, sun taimaka wajen cimma burin samar da guraban ayyukan yi guda biyu ga ko wane iyali."

Guan Ailing tana aiki ne, a wani kamfanin gyara tufaffi da garin ya shigo da shi. Dukkan ma'aikatan dake aiki a kamfanin mazauna al'ummar ne da kuma wadanda ke zama a kauyukan dake kusa da su. Guan Ailing ta gayawa wakilinmu cewa, kafin su soma aiki, al'ummar ta ba su horo na musamman, a lokacin samun horo, ko wanensu na iya samun kudin tallafi na RMB yuan 30 a ko wace rana. Guan Ailing ta ce,

"Na fara aiki, bayan kammala samun horo na kwanaki 15, a yayin da nake samun horo, ana ba RMB 30 a ko wace rana. Yanzu ina samun kudin shiga sama da1000 a ko wane wata."

Guan Ailing ta kara da cewa, idan aka kwatanta da sauran ma'aikata, kudin shiga da ta samu ba su da yawa, saboda mutum yana samun kudi ne bisa yawan ayyukan da ya yi, a cewar ta, idan ta kware a aikin, to yawan kudin da za ta samu zai kai sama da 3000. Yanzu dai Guan Ailing tana gamsuwa sosai kan yadda zaman rayuwarta yake, ta ce, kamfanin da take aiki na kusa da gidansu ne, kuma 'ya'yansu ba za su yi amfani da lokuta da yawa wajen tafi makaranta ba, mijinta ma na samun sauki wajen tafi aiki da mota. Ta ce,

"A baya, ba na samun kudin shiga ko kadan, yanzu ina samun yuan 1000 da wani abu, ko da yake ba su da yawa, amma za su taimaka mana mu biya bukatunmu na rayuwa dai dai gwargado. Ban da wannan kuma, makarantar na kusa da gida, hakika yanayin da muke ciki a yanzu ya fi na da nesa ba kusa ba."

Takardar bayani game da "Tusugunar da masu fama da talauci a wuraren da suka dace" da kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima na kasar Sin ya kaddamar a watan Maris na shekarar 2018, ta nuna cewa, a cikin shekara a 2016 zuwa 2017, yawan mutanen da suka ci gajiyar manufar tsugunar da masu fama da talauci a wuraren da dace a fadin kasar, ya kai kimanin miliyan 5.89. A shekarar 2018 kuma, akwai mutane kimanin miliyan 2.8 da suka kaura daga yankuna masu fama da talauci. Nan da shekarar 2020 kuma, za a cimma burin kawar da mutane masu fama da talauci dake zama a yankunan da ba su dace da rayuwa ba kwata-kwata.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China