2019-08-03 15:52:47 cri |
A cikin sanarwar, kwamitin sulhun MDDr ya bukaci a hanzarta kai dauki ga cutar Ebolar, saboda annobar za ta iya yaduwa cikin sauri, wanda zai iya shafar kasashen dake makwabtaka da yankunan kasar, lamarin da ake fargabar zai iya haifar da mummunan sakamako game da ayyukan jin kai, kuma zai shafi batun zaman lafiyar yankunan kasar baki daya.
Sanarwar ta kara da cewa, MDDr ta bayyana damuwa matuka game da yanayin tabarbarewar tsaro da ake ciki a yankunan da annobar Ebola ta shafa, musamman saboda yawan hare haren da ake kaiwa jami'an aikin ba da jin kan bil adama, da jami'an kiwon lafiya, wanda hakan yana matukar gurgunta ayyukan jami'an kiwon lafiyar, lamarin da zai kara haddasa yaduwar kwayoyin cutar Ebola a sauran yankunan kasar ta Kongo. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China