Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon jakadan Sin a MDD: Kasar Sin za ta kare tsaro da yankunanta da ma yancinta na samun ci gaba
2019-07-31 11:09:57        cri

Sabon wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD, Zhang Jun ya bayyana kudirin kasarsa na kare 'yanci da muradun kasashe masu tasowa.

Jakada Zhang Jun ya bayyana hakan ne, a rana ta farko da kama aiki a matsayin wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD. Ya ce, a 'yan shekarun da suka gabata, kasashe masu tasowa sun samu nasarori a fannin ci gaba, a hannu guda kuma suna fama da jerin kalubale da matsaloli na rashin daidaito na ci gaba.

Ya ce, duk da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin ci gaba, amma har yanzu tana fama da wasu matsaloli na rashin wasu abubuwa da rashin daidaito na ci gaba a wasu fannoni. Kuma har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa.

Jami'in na kasar Sin ya kuma soki yadda wasu kasashe, ke furta wasu kalaman da ba su dace ba game da matsayin kasar Sin na kasancewa kasa mai tasowa. Yana mai cewa, kasar Sin tana adawa da duk wata kasa dake amfani da matsayin kasa mai tasowa, wajen haifar da tsaiko ga ci gabanta ko kokarin take mata 'yanci.

Don haka, a cewarsa, kasar Sin za ta nace wajen kare tsaro da yankunanta da ma 'yancinta na neman bunkasuwa cikin lumana. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China