Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin da kasar Sin ta samu daga wasu fannoni uku na tattalin arziki ya dau kaso 16.1% na GDP
2019-07-29 13:14:14        cri
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a jiya Lahadi sun nuna cewa, a shekarar 2018, yawan kudin da kasar ta samu daga wasu sabbin fannoni uku na tattalin arziki ya kai kimanin yuan trilliyan 14.5, adadin da ya dau kaso 16.1% na ma'aunin GDP na kasar, wanda kuma ya karu da kaso 0.3% bisa na makamancin lokacin bara.

A cewar hukumar, wadannan sabbin fannoni uku sun hada da sabbin masana'antu da aka kirkiro a sakamakon sabbin nasarorin da kasar ta samu a fannin nazarin kimiyya da fasaha, sai kuma sabbin sassan harhada kayayyaki da suka bullo don biyan karin bukatun kayayyaki da hidimomi ta fannoni daban daban. Baya ga haka, akwai kuma fannin sabon tsarin kasuwanci da aka kafa domin kara inganta harkokin kasuwanci. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China