Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta mayar da martani game da budaddiyar wasikar Amurka
2019-07-26 14:00:45        cri

Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin MOC ta ce, takaddamar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ba zai taba samun goyon bayan al'ummar Amurka ba, yayin da hadin gwiwar cin moriyar juna tsakanin bangarorin biyu shi ne babban abin da jama'ar kasashen biyu suke muradi.

Kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin \ ya furta hakan a cikin martanin budaddiyar wasikar da wasu Amurkawa sama da 100 suka aikewa shugaban kasar Amurkar Donald Trump, inda suka bukaci gwamnatin Amurka da ta tsaya tsayin daka kan aniyarta na kalubalantar kasar Sin. Kakakin ya ce, ana fatan wasu Amurkawa za su kara azama kan hadin gwiwar cin moriyar juna maimakon yunkurin ta da takaddama da neman yin kama karya.

A cewar kakakin na MOC, wasikar, wacce wasu tsoffin sojoji da tsoffin jami'an tattara bayanan sirri na Amurka suka sanya wa hannu, cike take da tunani irin na danniya da yakin cacar baka marar tushe, inda aka bata sunan kasar Sin ta fuskar manufofin cikin gida da manufofin diplomasiyya, a ingiza kasashen 2 mafiya karfin tattalin arziki a duniya su rabu da juna ta fuskar tattalin arziki, kana kuma a nemi ta da jijiyar wuya da kuma haifar da rashin jituwa tsakanin kasashen biyu.

Ma'aikatar ta lura cewa, wasu kwararrun Amurka 100 daga bangarorin siyasa, soji, masana'antu, kasuwanci, da malaman jami'o'i su ne suka hadu suka rubuta wata budaddiyar wasika ta daban mai taken "Kasar Sin ba abokiyar gaba ba ce" a watan da ya gabata.

Daga cikin martani daban daban daga kafafen yada labarai da jama'ar kasashen biyu na martanin da suka mayar kan wasikun guda biyu, ana iya fahimtar cewa, yunkurin ta da takaddama da yin fito-na-fito tsakanin Sin da Amurka bai samu goyon bayan mafi yawan jama'ar kasar Amurka ba. Kakakin ya kara da cewa, kokarin karfafa dangantakar cin moriyar juna tsakanin kasashen biyu shi ne babban abin da jama'ar kasashen biyu suka fi amincewa da shi kuma suka fi bukata.

A cewar kakakin, a ko da yaushe kasar Sin ta yi amanna cewa, hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka batu ne na kyautata moriyar juna. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China