Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba za a amince wasu kasashen waje su tada rikici a yankin Hong Kong ba
2019-07-24 13:48:34        cri

Game da tashe tashen hankula da suka faru a kwanakin baya a yankin Hong Kong, wasu jami'an Amurka da Birtaniya sun bayyana ra'ayoyi marasa tushe, inda suka ce, wai ya kamata gwamnatin yankin Hong Kong ta girmama 'yancin fadin albarkacin baki da na yin zanga-zanga, ta kuma tabbatar da ikon tafiyar da harkokin yankin da kansa da sauransu. Wadannan kalaman banza sun saba wa hakikanan abubuwa, da nuna goyon baya ga masu kin babban yankin kasar Sin, da masu tada rikici a yankin Hong Kong, da harzuka manufar "kasa daya amma da tsarin mulki biyu", baya ga tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin. Don haka Sin nuna matukar rashin jin dadinta da kuma kin amincewa da batun.

Yankin Hong Kong yanki ne da ake tafiyar da harkokinsa bisa dokoki. Ana tabbatar da 'yanci da hakkin mazauna yankin, a fannonin fadi albarkacin baki da yin zanga-zanga. Amma yayin da jama'ar yankin suke yin amfani da wadannan hakkokin, ya kamata su rika girmama hakkin sauran jama'a, kana bai kamata a kawo illa ga odar yankin, da kuma aikata laifuffuka ba.

A kwanakin baya, wasu masu tsattsauran ra'ayi sun kutsa cikin babban ginin majalissar dokokin yankin Hong Kong, suka kai hari ga 'yan sanda, da tsare kofar ofishin wakilin gwamnatin tsakiyar kasar dake yankin Hong Kong, tare da bata tambarin kasa dake kofar ofishin da wasu launuka, wadannan munanan ayyukan nuna karfin tuwo sun wuce 'yancin da ake bai wa jama'a na fadi albarkacin baki da yin zanga-zanga cikin lumana, wadanda suka kasance tsokana da ake nuna wa dokokin yankin, da manufar "kasa daya tsarin mulki biyu" da ma kwarjinin gwamnatin tsakiyar kasar Sin. Don haka babu wata kasa da za ta iya yin hakuri da irin wannan batu. Yadda 'yan sandan yankin Hong Kong sun daidaita rikici bisa doka, na iya tabbatar da kwanciyar hankali a yankin tare da kare martabar yankin na tafiyar da harkokinsa bisa doka.

A hakika dai, kasashen yammacin duniya musamman kasar Birtaniya ba su cancanci ambato 'yancin fadi albarkacin baki da yin zanga-zanga a yankin Hong Kong ba. A yayin da kasar Birtaniya ta mallaki yankin Hong Kong, ko mazauna yankin suka samu ikon tafiyar da harkokinsu da kansu? A cikin shekaru 22 bayan da yankin Hong Kong ya dawo kasar Sin, bisa tsarin mulkin kasar da dokokin yankin Hong Kong, gwamnatin kasar Sin ta aiwatar da manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu", da ta "jama'ar yankin Hong Kong su sarrafa harkokin yankin da kansu" a tsanake. Hakan ya sa al'ummun yankin sun samu hakkin demokuradiyya da 'yanci da ba su taba samu a baya ba. Kana yawan GDP na yankin ya karu daga kudin Hong Kong biliyan 1370 a shekarar 1997 zuwa biliyan 2840 a shekarar 2018. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu", hanya ce mafi dacewa ta warware matsalar yankin, da kiyaye samun wadata da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Kasa daya shi ne tushen manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu". Kamar yadda Sinawa su kan ce, idan babu gindin bishiya mai inganci sai babu yawan ganyayenta. Idan babu babban yankin kasar Sin, ba za a samu ci gaba kamar haka a yankin Hong Kong ba. Gwamnatin kasar Sin tana da ikon tafiyar da harkokin yankin a dukkan fannoni, ba kuma za a amince da duk wani yunkurin da ya sabawa ikon gwamnatin tsakiyar kasar ba bisa hujjar wai tafiyar da mulkin hongkong cikin 'yanci sosai. Yadda wasu 'yan siyasa na kasar Amurka da na Birtaniya suka zargi aikin gwamnatin kasar Sin na tafiyar da harkokin yankin Hong Kong yadda ya kamata, a matsayin tsoma baki kan hakkin tafiyar da harkokin yankin da kansa, ya kyale wani hakikanin al'amarin, wato harkokin da suka shafi yankin Hong Kong harkoki ne na cikin gidan kasar Sin.

Bisa labaran da kafofin watsa labaru suka bayar a kwanakin baya, za a iya gano cewa, wasu kasashen waje ne suka tsara, da gudanar da ayyukan tada rikice-rikice a yankin Hong Kong. Ganin yadda wasu 'yan siyasa kalilan na kasashen yammacin duniya kamar Amurka da Birtaniya, suka goyi bayan masu kin amincewa da Sin da masu ta da kura a Hong Kong a fili, kana wasu kananan ofisoshin jakadancin kasashen suka hura wuta kan mummunan batun ba tare da kula da dokokin kasa da kasa da ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, gami da 'yan sandan Hong Kong suka kama wasu mutane masu dauke da boma-bomai nau'in TATP, wadanda daya daga cikinsu ke da alaka da 'yan ta'adda na kasashen waje. Lamarin da ya shaida cewa, hargitsin da ya faru a yankin ba su da nasaba da 'yancin mazauna yankin na fadi albarkacin baki da da yin zanga-zanga cikin lumana, a maimakon hakan, babban laifin karya doka ne na nuna tsattauran ra'ayi da kasashen waje suka gudanar tare da wasu mutanen yankin.

Tun daga batun yin zanga-zanga a farfajiyar Central dake yankin Hong Kong ba bisa dokoki ba a shekarar 2014, har zuwa babban lafin ta da rikici da ya faru a kwanakin baya a yankin, ake iya ganon cewa, ko da yaushe wasu kasashen waje ke yunkurin tada rikice-rikice a yankin ne don kawo illa ga manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu", da kuma neman samun ikon sarrafa yankin, da tada zaune-tsaye a yankin Hong Kong, har ma da dukkan kasar Sin baki daya. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China