2019-07-14 17:44:53 cri |
Bankin AIIB, sabon bankin bangarori daban daban ne dake kula da zuba jari ga ayyukan more rayuwa, cibiyarsa tana birnin Beijing. Tun daga shekarar 2016 da aka bude shi, an fadada membobin bankin sau 9, yawan membobin bankin ya karu daga 57 zuwa 100, yawancinsu kasashe masu tasowa ne, amma akwai wasu kasashe masu karfin ci gaba kamar su Birtaniya, Faransa, Jamus, Canada da sauransu.
A cikin shekaru fiye da 3 da suka gabata, bankin AIIB ya kyautata aikin gina ayyukan more rayuwa don kara samar da damammakin bunkasuwa ga tattalin arzikin nahiyar Asiya har ma dukkan duniya baki daya, wanda ya samu nasarori da dama. Na farko, bankin AIIB ya biya bukatun kasashen masu tasowa na tattara kudi don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikinsu. A halin yanzu, bankin AIIB ya tattara kudi dala biliyan 8 da miliyan 500 ga ayyuka 46 na kasashe 18 a duniya, wadanda suka shafi fannonin sufuri, makamashi, sadarwa, bunkasa birane da sauransu, yawancin ayyukan za a gudanar da su ne a nahiyar Asiya. Na biyu, bankin AIIB ya biya bukatun zuba jari na membobin bankin ciki har da kasashen da suka ci gaba. An ce, ana bukatar jarin da za a zuba ga nahiyar Asiya a fannin gina kayayyakin more rayuwa a kowace shekara da ya kai dala biliyan 1400, kana ga nahiyar Afirka shi ne dala biliyan 68 zuwa 108. Kasashen da suka ci gaba za su iya zuba jari ga Asiya da Afirka ta hanyar bankin AIIB wajen ayyukan gina kayayyakin more rayuwa don more damar samun bunkasuwar tattalin arziki tare.
Dalilin da ya sa aka nuna yabo ga bankin AIIB shi ne ya samar da sabuwar gudummawa ga tsarin sarrafa tattalin arzikin duniya. Bankin duniya da asusun ba da lamini na IMF da sauran hukumomin hada-hadar kudi na duniya ba su iya gabatar da hakikakin yanayin sabbin kasashe mafiya samun bunkasuwar tattalin arziki da kasashe masu tasowa ba, amma bankin AIIB yana da yawancin membobinsa ne daga kasashe masu tasowa, don haka za a sa kaimi ga raya tsarin sarrafa tattalin arzikin duniya cikin adalci yadda ya kamata.
Bankin AIIB banki ne na hadin gwiwar hada-hadar kudi ta duniya bisa kiran da Sin ta yi, kana shi ne dandalin kasa da kasa da Sin ta samarwa dukkan duniya. A yayin da aka bude bankin, kasar Sin ta yi alkawarin nuna goyon baya ga raya bankin AIIB, ban da gabatar da kudinta a cikin bankin cikin lokaci, kana ta ba da dala miliyan 50 ga bankin don kafa asusun bude sabbin ayyukan bankin, da nuna goyon baya ga kasashe marasa ci gaba wajen gina ayyukan more rayuwa. A cikin shekaru fiye da 3 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta cika alkawarinta bi da bi, kana ba ta tsoma baki kan harkokin bankin AIIB, kuma ba ra'ayin kasar Sin kadai ake saurara a yayin tsaida kudurin bankin ba. Hakan ya tabbatar da cewa, bankin AIIB yana gudanar da ayyukansa bisa ka'idojin hukumomin kasa da kasa, kuma ya kara janyo hankalin kasa da kasa.
Yawan membobin bankin AIIB ya karu daga 57 zuwa 100, hakan ya shiga sabon lokaci a tarihin bankin. Ana fatan bankin AIIB zai ci gaba da gudanar da ayyukansa bisa ma'aunin koli, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin Asiya da duniya, da kuma kara samar da gudummawa ga sarrafa tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China