2019-07-14 15:09:42 cri |
A ranar Asabar shirin hadin gwiwar kungiyar tarayyar Afrika AU da MDD ya sanar da aniyarsa na karrama matan Afrika bisa irin rawar da suke takawa ta fuskar taimakawa ci gaban rayuwar mata da raya ajandar zaman lafiya da tsaro a fadin Afrika.
Lambobin yabon, wani bangare ne na hadin gwiwar AU da MDD kan al'amurran ci gaban mata, da shirin zaman lafiya da tsaro a Afrika, ana sa ran za'a kaddamar da shirin ne a gefen taron kolin AU karo na 33, wanda za'a gudanar a watan Fabrairun shekarar 2020 a helkwatar kungiyar tarayyar Afrika dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Kungiyar mai mambobin kasashen Afrika 55, ta bukaci a zabo matan Afrika da suka yi fice wajen bunkasa rayuwar mata, da tallafawa ajandar samar da zaman lafiya da tsaro a Afrika domin shigar da su cikin muhimmin shirin raya ci gaban nahiyar, wanda ya kasance na hadin gwiwa ne tsakanin AU da ofishin MDD mai kula da kungiyar tarayyar Afrika wato (UNOAU).
Bikin ba da lambar yabon na nahiyar zai mayar da hankali ne wajen karrama matan Afrika da suka yi fice wajen tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China