Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana sun yi kira ga kasashen Sin da Amurka da su zurfafa alaka a tsakaninsu
2019-07-10 20:15:32        cri
Wasu masanan kasar Amurka sun yi kira ga Sin da Amurka, manyan kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, da su zurfafa alaka don ci gaba da cin moriyar juna, maimakon yin fito-na fito da zai haifar da yanayi na yin hasara.

Stephen Roach, babban jami'i a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Jackson dake jami'ar Yale ta kasar Amurka, ya shaidawa kamfabin dillancin labarai na Xinhua a gyefen taron dandalin kasa da kasa mai taken, "alakar Sin da Amurka a fannin ciniki da tattalin arziki, mene ne a yanzu, me zai biyo baya" taron da ya gudana a Hong Kong, inda ya ce, yanzu ba lokaci ne na yin fito na fito ba, yanzu lokaci ne da za a kaucewa abun da shugaban kasar Amurka ke yi, a wani tsari da sunan cimma wata yarjejeniya inda wata kasa za ta yi kokarin yi wa wata kasa barazana.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China