![]() |
|
2019-07-10 10:13:04 cri |
Ma'aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce bisa gayyatar da aka yi masa, mataimakin firaministan kasar Liu He, ya tattauna ta wayar tarho jiya da yamma, da wakilin Amurka kan harkokin cinikayya, Robert Lighthizer da sakataren ma'aikatar kudi ta kasar, Steven Mnuchin.
Liu He, wanda kuma mamba ne na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma jagoran wakilan kasar Sin dake tattauna batun cinikayya da Amurka, ya yi musayar ra'ayi da wakilan na Amurka game da aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin ganawar da suka yi a gefen taron koli na kungiyar G20 da aka yi a birnin Osaka na kasar Japan. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China