2019-07-10 09:21:45 cri |
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce, an kama masu zanga-zanga 40, mabiya darikar Shi'a, bayan kutsa kai da suka yi cikin harabar majalisar dokokin kasar.
Zanga zangar mabiya Shi'ar ta neman sakin shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa dake tsare, ta rikide zuwa rikici ne bayan daruruwan masu zanga zangar sun kutsa harabar majalisar dokokin kasar dake birnin Abuja.
Kakakin rundunar 'yan sandan Anjuguri Manzah, ya ce masu zanga-zangar sun harbi 'yan sanda 2 a kafa, yayin da jefan da suka yi da duwatsu suka raunata wasu 'yan sandan 6.
Anjuguri Manzah ya ce, 'yan sandan da suka jikkata na cinya a wani asibiti dake birnin.
Wata 'yar jarida da lamarin ya auku a kan idonta, Titilope Fadare, ta ce rikicin ya katse harkokin kasuwaci a kewayen ginin majalisar, inda masu zanga-zangar suka kone motoci 2 da lalata wasu 3. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China