2019-07-09 11:01:25 cri |
Ma'aikatar ta ce a birane 337 da ta nazarta, matsakaicin kyawun iskar su ya kai kaso 80.1 bisa dari cikin watannin 6, wanda hakan ke nuna karuwar ingancin iskar da kaso 0.4 a shekara guda.
Kaza lika alkaluman da MEEn ta fitar a jiya Litinin, sun nuna cewa, matsakaicin karuwar awon gurbatar iska na PM2.5 da aka samu a biranen ya ragu, da kaso 2.4 bisa dari a shekara guda, wanda a tsakanin lokacin bai wuce "micrograms 40" a kan kowace "cubic meter" ba. Yayin da kuma yawan matsakaicin sinadarin "sulfur dioxide" da PM10 dake cikin iska suka yi kasa, zuwa kaso 4.2 da kaso 14.3 bisa dari.
An danganta kyautatuwar iska a biranen ne, da namijin aikin da gwamnati ke yi a fannin yaki da gurbatar iska da lalacewar muhalli.
A wani ci gaban kuma, ma'aikatar kare muhallin ta alkawarta sake kaddamar da zagaye na gaba, na sanya ido kan ingancin muhalli, wanda karkashinsa, masu aikin sanya ido za su ziyarci larduna 6, tare kuma da wasu manyan kamfanoni biyu, dake karkashin kulawar gwamnatin tsakiyar kasar. (Saminu Hassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China