Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar AfCFTA ta fara aiki a hukumance
2019-07-08 10:21:00        cri

A jiya Lahadi shugabannin kasashen Afrika suka kaddamar da fara aiki da yarjejeniyar ciniki maras shinge ta kasashen Afrika wato (AfCFTA) a hukumance a birnin Niamey.

An kaddamar da fara aiki da yarjejeniyar ne a lokacin kaddamar da taron kolin shugabanin kasashen mambobin kungiyar (AU) karo na 12 a Niamey, babban birnin jamhuriyar Nijer.

Shugaban gudanarwa kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yaba da kaddamar da yarjejeniyar, inda ya bayyana cewa, tana da babbar ma'ana ce a tarihin kasashen Afrika, musamman a yunkurin tabbatar da burin ajandar shekaru 50 ta raya nahiyar Afrika nan da shekarar 2063.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, wanda shi ne ya shugabanci taron AU na wannan karo, ya bayyana ranar Lahadi da cewa, mai matukar muhimmanci ce ga yunkurin Afrika na neman bunkasa ciniki da kasuwanci da daga martabar yankin.

Mataimakiyar babban sakataren MDD Amina Mohammed ta ce, fara aiki da yarjejeniyar ciniki maras shinge al'amari ne mai cike da tarihi ga Afrika. Ta bukaci kasashen Afrika su yi kokarin cin gajiyar dake tattare da shirin yarjejeniyar cinikin.

An kaddamar da yarjejeniyar ta AfCFTA ne, a ranar 21 ga watan Maris a bara a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, kuma a ranar Lahadi Najeriya kasa mafi yawan al'umma da karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika, da jamhuriyar Benin suka rattaba hannu kan yarjejeniyar, yayin da Eritrea ce kasa daya tilo cikin mambobin kungiyar tarayyar Afrika 55 da ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba kawo yanzu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China