Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na son kara tattaunawa da kasashen Afirka wajen daidaita matsaloli yadda ya kamata
2019-07-03 20:03:48        cri

A yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya ce kasar Sin da kasashen Afirka, suna gudanar da ayyukan hadin gwiwa da dama, inda kuma aka samu nasarori masu tarin yawa, ko da yake an samu wasu matsaloli yayin da ake gudanar da ayyukan.

Ya ce kasar Sin na son kara tattaunawa da kasashen Afirka masu ruwa da tsaki, bisa ka'idar girmamawa, da yin shawarwari yadda ya kamata. An yi imanin cewa, za a lalubo bakin zaren daidaita matsalolin ta hanyar da ta dace.

Rahotanni sun ce, a kwanan baya, an samu matsaloli yayin da kasashen Sin da Tanzaniya, da Kenya, suke gudanar da wasu ayyukan hadin gwiwa. Sa'an nan mujallar masu ilmin tattalin arziki ta "The Economist" ta kasar Birtaniya ta labarta cewa, wai ba a gamsu da sakamakon wasu ayyukan hadin gwiwar Sin da Afirka ba. Kana kasashen Afirka sun fara yin taka tsan-tsan, kan tarkon basusuka da kasar Sin ta yi musu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China