Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bullo da manufofin taimakawa yankuna masu fama da tsananin talauci
2019-06-26 20:24:42        cri

Mataimakin darektan ofishin kawar da talauci da raya kasa na kasar Sin, Ou Qingping ya bayyana cewa, kasarsa ta himmatu wajen taimakawa yankunan dake fama da matsanancin talauci, yayin da wa'adin da kasar ta Sin ta tsayar na kawar da talauci baki daya daga fadin kasar nan da shekarar 2020 ke karatowa.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a yau, ya ce, daga shekarar 2018 zuwa 2020, gwamnatin tsakiya za ta ware Yuan biliyan 214, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 31 ga irin wadannan yankunan, ciki har da yankin Tibet mai cin gashin kansa da wasu sassan jihar Xinjiang na kabilar Uygur mai cin gashin kanta, inda har yanzu ake fama da kangin talauci.

Ya ce, baya ga kudaden tallafin, har ila gwamnati ta kara kokarin janyo kamfanoni masu zaman kansu 76,400 a fannin kawar da talauci, matakin da ya amfani sama da mutane miliyan 10. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China