Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Zimbabwe ta haramta amfani da kudaden ketare a matsayin kudaden hada-hadar kasuwanci a kasar
2019-06-25 13:33:37        cri
Gwamnatin Zimbabwe ta haramta amfani da kudaden ketare a matsayin kudin hada-hadar kusuwanci a kasar, a wani yunkuri na dakile karuwar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum da sauran kayayyaki da hidimomi.

Sai dai, haramcin bai shafi biyan kudin hidimomin kamfanonin jiragen sama na kasashen waje ba.

Ministan harkokin kudi da tattalin arziki na kasar Mthuli Ncube ne ya sanar da haramcin a jiya Litinin, inda ya ce wannan na nufin dalar Zimbabwe wanda ke daidai da dalar RTGS da takardu da kwandalar lamuni, su ne kadai wadanda aka amince a yi amfani da su, yana mai cewa haramcin ya fara aiki ne nan take. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China