![]() |
|
2019-06-14 10:34:04 cri |
A jawabin da ya gabatar a wajen taron wuni uku na dandalin makamashi da hakar ma'adanan Ghana na shekarar 2019, Adam ya ce, kasancewar tattalin arzikinsu ya dogara ne kacokan kan hakar ma'adanai, yana da matukar muhimmanci ga gwamnatin kasar ta ta yi hobbasa wajen mayar da fanni a matsayin wani bangare dake matukar janyo hankalin masu zuba jari.
"A halin da ake ciki yanzu bisa ga tarihin ci gabanmu, yana da matukar muhimmanci gare mu mu zurfafa kan irin gudunmowar da hakar ma'adanai da makamashi ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikinmu kuma mu yi kokarin bunkasa ci gaban kasarmu," in ji shi.
Ghana tana daya daga cikin kasashen duniya mafiya samar da zinare a nahiyar Afrika.
A cewar Adam, gwamnati tana daukar bangaren hakar ma'adanai a matsayin kamfanonin da aka fi samun takara wanda kuma ya dogara ne kan lantarki a matsayin babban mai ruwa da tsaki a fannin makamashin kasar.(Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China