Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron masu sauraro da kallon shirye-shiryen "Kalaman Xi Jinping" a kasar Rasha
2019-06-07 16:58:31        cri

A jiya ne, aka gudanar da taron masu sauraro da kallon shirye-shiryen "Kalaman Xi Jinping" a gidan rediyon Metro na Saint Petersburg dake kasar Rasha, inda mataimakin shugaban ma'aikatar yayata manufofin kasar Sin, kuma shugaban CMG Shen Haixiong, da manazarcin shugaban kasar Rasha mai kula da tattalin arziki Sergey Glaziev, da wakilai fiye da 100 na bangarori daban daban ciki har da na gwamnatoci, da masana'antu, da cinikayya, da kafofin watsa labaru da sauransu suka halarci taron.

Shen Haixiong ya bayyana a gun taron cewa, hadaddiyar sanarwa game da raya dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a sabon zamani a tsakanin Sin da Rasha wadda shugaban Sin Xi Jinping da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vlładimir Putin suka sa hannu tare ta shaida cewa, an shiga sabon lokaci na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. An gabatar da shirye-shiryen "Kalaman Xi Jinping" da yaren Rashanci a kasar Rasha, wadanda suka samu karbuwa sosai, wanda ya bayyana cewa, ana da kyakkyawan makoma kan hadin gwiwar dake tsakanin kafofin watsa labaru na kasashen biyu. Tunanin sarrafa harkokin kasa da siyasa da shugaba Xi Jinping ya bayyana a cikin shirye-shiryen ya taimakawa masu sauraro da kallo na kasashen waje su kara fahimtar kasar Sin na halin yanzu.

A nasa bangare, Glaziev ya yi nuni da cewa, yayin da Sin da Rasha suke yin mu'amala da juna, ana fahimtar juna a tsakaninsu. Ya ce, gaskiya da adalci su ne tushen al'adu na kasashen biyu. Don haka, shirye-shiryen "Kalaman Xi Jinping" na yaren Rashanci sun jawo hankalin jama'ar kasashen biyu sosai. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China