Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiar St. Petersburg ta baiwa shugaban Sin digirin girmamawa
2019-06-07 15:52:35        cri

Jami'ar St. Petersburg ta kasar Rasha, ta karrama shugaban kasar Sin Xi Jinping, da digirin girmamawa a jiya Alhamis, yayin bikin musamman da shugaba Vladimir Putin ya halarta.

A jawabin sa bayan karbar digirin na girmamawa, shugaba Xi ya ce yana alfahari da wannan karramawa da jami'ar St. Petersburg ta yi masa. Ya ce hadin gwiwa a fannin ilimi, muhimmin mataki ne dake taimakawa wajen karfafa fahimtar juna da kawance.

A cewar shugaban na Sin, hadin gwiwa da musaya tsakanin jami'ar da takwararta ta Sin, ya bunkasa musayar al'adu tsakanin kasashen biyu, da ma nazarin da ake yi na al'amuran Rasha a kasar Sin.

Da ya tabo batu game da digirin girmamawa da jami'ar Tsinghua dake Sin ta baiwa shugaban Putin a watan Afrilun da ya shude, shugaba Xi ya ce jami'o'in Tsinghua da St. Petersburg, manyan wakilai ne a fannin raya ilimi a kasashen Sin da Rasha. Kuma digirin girmamawa da suka baiwa shugabannin kasashen juna, na nuni ga irin musayar ilimi, da al'adu, dake wanzuwa tsakanin kasashen biyu. Ya kuma nuna mataki na kusanci a fannin musaya tsakanin kasashen biyu.

Daga nan sai shugaban na Sin ya bayyana fatan cewa, kasashen biyu za su ci gaba da fadada musaya da hadin kai, da yayata kyawawan al'adun su. Su kuma yi koyi da juna, ta yadda za su ci karin gajiyar ci gaba daga kwarewar su.(Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China