Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron koli na kungiyar OIC
2019-06-01 15:34:29        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sako don taya murnar bude taron koli na kungiyar hadin kai ta kasashen musulmi ta (OIC) a birnin Makka.

A cikin sakon da ya aike a jiya, Xi Jinping ya nuna cewa, kungiyar OIC alama ce ta hadin kan kasashe masu bin addinin musulunci, kuma cikin shekaru 50 da kafa kungiyar, ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan kasashen musulumi, yana mai yaba mata sosai kan wannan.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin da kasashen musulumi na da kyakkyawar huldar abota tun fil azal, kuma a ko da yaushe, bangarorin biyu na goyon bayan juna, da gudanar da hadin kai da zuciya daya. Ya ce Kasar Sin na mayar da hankali sosai kan sada zumunci da kasashen OIC, kuma tana mayar da kungiyar a matsayin gada tsakanin bangarorin biyu wajen hadin kai. Kana kasar Sin na fatan hada hannu da kasashen don kara amincewa juna a fannin siyasa, da inganta kawance da sa kaimi kan tattaunawa, ta yadda za a kafa makomar dangantakar tsakanin Sin da duniyar Islama mafi kyau a nan gaba, da taka rawa kan kafa kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China