Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin masana'antu na kasar Habasha da Sin ke ginawa, ya ja hankalin manyan kamfanonin hada magunguna na duniya
2019-05-28 10:16:08        cri
Gwamnatin Habasha, ta bayyana cewa, yankin masana'antun kasar na Kilinto da kasar Sin ke aikin ginawa, ya bunkasa burin kasar na jan hankalin manyan kamfanonin hada magunguna na duniya.

Hukumar kula da zuba jari ta Habasha (EIC), ta bayyana a jiya cewa, ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin zuba jari da kamfanonin kasa da kasa 10, wadanda suka nuna sha'awar kafa masana'antunsu a harabar yankin masana'antun na Kilinto.

Hukumar ta bayyana cewa, da zarar an kammala yankin na Kilinto, zai kara karfin yankin gabashin Afrika na jan hankalin kamfanonin kasashen waje a fannin hada magunguna.

Kafar yada labarai ta FBC ta kasar, ta ruwaito mataimakin kwamishinan hukumar EIC, Temesgen Telahun na cewa, ana gab da kammala ginin yankin na Kilinto, kuma idan aka gama, zai dauki kamfanonin hada magunguna sama da 1,000.

Kamfanin gine gine ne kasar Sin na Tiesiju Civil Engineering Group LTD ne ke aikin ginin yankin masana'antun na Kilinto da ya mamaye fili mai fadin kadada 270 a wajen Addis Ababa babban birnin kasar Habasa, a kan kudi dala miliyan 204. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China