Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zimbabwe da Kasar Sin za su gaggauta aiwatar da ayyukan hadin gwiwa karkashin tsarin FOCAC
2019-05-25 16:08:51        cri
Zimbabwe da kasar Sin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin gaggauta aiwatar da ayyukan hadin gwiwa a tsakaninsu.

Mataimakin ministan kula da cinikayya na kasar Sin dake ziyara a Zimbabwe, Qian Keming ne ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin kasarsa, yayin da Ministan harkokin wajen Zimbabwe Sibusiso Moyo ya rattaba a madadin tasa kasar.

Kasashen biyu na son inganta aiwatar da matakan bunkasa cinikayya da tattalin ariki da suka amince da su karkashin tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar Sin dake Harare ya fitar a jiya bayan ganawar da aka yi tsakanin ministocin biyu, ta ce bangarorin biyu sun amince su bunkasa hadin gwiwa a bangarori da dama.

Sibusiso Moyo, ya ce ta hanyar hadin gwiwa da kasar Sin, Zimbabwe na son aiwatar da ayyukan da jama'a za su ci gajiyarsu, wadanda kuma ba za su kuntatawa matsayin kasar na biyan bashi ba.

Ya ce Zimbabwe na son fadada hadin gwiwarta da kasar Sin a fannin hada-hadar kudi, ta yadda za ta daidaita bangarenta na hada-hadar kudi da a yanzu ke fama da karancin kudi da matsalar musayar kudaden ketare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China