Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Domin tabbatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya", kasar Sin ta taimakawa manoma mata a kasar Nepal wajen kawar da talauci
2019-05-20 14:49:12        cri

Masu sauraro, a ranar 25 ga watan Afrilu na shekarar 2015 ne, wata mummunan girgizar kasa mai karfin maki 8.1 ta aukawa kasar Nepal, da jin wannan labari, sai asusun kawar da talauci na kasar Sin ya tattara kudi cikin sauri, ya kuma aika wata tawaga zuwa kasar don gudanar da ayyukan ceto na gaggawa da sake raya kasar bayan bala'in. Bayan da aka kammala matakin farko na aikin, bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya" da manufar kafa kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil Adama, sai asusun ya bude ofishinsa a kasar ta Nepal a watan Agustan shekarar 2015, don soma aikin sake raya kasar da kuma sauran ayyukan kawar da talauci.


A cikin shekaru kusan hudu da suka gabata, ofishin ya himmatu wajen raya fasahohin da kasar Sin ta samu a fannoni guda hudu, ciki har da sake raya kasa bayan bala'i, kawar da talauci, kiwon lafiya da kuma ba da ilmi mai inganci a kasar ta Nepal, irin hidimar da ya samarwa jama'ar wurin ta sanya an samu moriya a fannonin tattalin arziki da al'umma. Cikin wadannan ayyuka, aikin samar da kananan rancen kudi da ake aiwatarwa don taimakawa jama'ar wurin wajen kawar da talauci, ya kasance irinsa na farko da kasar Sin ta aiwatar a kasashen ketare. To, masu sauraro, a yau za mu kawo muku bayani ne game da wannan batu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China