Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na shirin bunkasa raya yankunan karkara ta hanyar fasahohin zamani
2019-05-17 15:09:49        cri
Kasar Sin na shirin inganta amfani da fasahohin zamani a yankunan karkara domin bunkasa ci gabansu.

A cewar takardar ka'idoji da ofishin kwamitin tsakiya na JKS da majalisar gudanarwar kasar suka fitar, a yunkurin zamanantarwa da sauya yankunan karkara, amfani da fasahohin zamani zai taka muhimmiyar rawa wajen farfado da su da gina kasar Sin irin ta zamani.

Takardar ta ce, kasar ta ci alwashin cimma bunkasa kauyuka zuwa na zamani ya zuwa shekarar 2020, inda za a samar da tsarin sadarwa na 4G ga kaso 98 na manyan kauyuka da kuma gaggauta raya tattalin arziki irin na zamani a yankunan karkara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China