Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bada rahoton samun karuwar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2019-05-17 10:07:39        cri
Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross, ta ce an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a makonnin baya-bayan nan, tana mai cewa ya kamata kasa da kasa su gagggauta kara kai dauki.

Daraktan sashen lafiya da kulawa na kungiyar, Emmanuele Capobianco, ya bayyana a jiya, yayin wani taron manema labarai na MDD a Geneva cewa, duk da nasarorin da aka samu na takaita bazuwar cutar, an samu sabbin wadanda suka kamu da ita a 'yan makonnin da suka wuce.

Bisa alkaluma daga ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar, kungiyar ta ce kaso 20 cikin mutane 1,671 da suka kamu da cutar ya zuwa ranar 11 ga watan nan, sun kamu da ita ne cikin makonni 3 da suka gabata.

A cewar kungiyar, tun bayan barkewar cutar Ebola a watan Augustan 2018, ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,000, inda ta zama barkewar cutar mafi muni na biyu a tarihi.

Emmanuele Capobianco ya ce aikin yaki da cutar na fuskanta matsaloli 2 da suka hada da karancin kudi da rashin tsaro. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China