Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bukaci a karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu a fannin hada-hadar kudi a Afirka
2019-05-10 09:42:36        cri

Babbar sakatariyar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD, Vera Songwe, ta jaddada bukatar kafa hadin gwiwa mai karfi tsakanin gwamnati da bangarori masu zaman kansu, domin bunkasa bangaren hada-hadar kudi a nahiyar Afrika.

Vera Songwe ta ce har yanzu ba a yi bayanin yanayin hadin gwiwar yadda ya kamata ba, inda ta ce ana bukatar aiki mai yawa daga dukkan bangarorin 2, domin fahimtar alfanun dake tattare da hadin gwiwar. Tana mai cewa, wajibi ne a bayyanin hadin gwiwar sosai tare da aiki da ita yadda ya kamata.

Ta ce bangare daya cikinsu ba zai iya samar da kudin ayyukan raya kasa ba, tana mai cewa, akwai bukatar fahimtar yanayin samar da kudade daga bangarori daban daban da sabbin rukunonin kadarori, yayin da ake magance matsin dake cikin hadin gwiwar, wanda ke bukatar hadaka da dama domin cin gajiyarta yadda ya kamata a muhimman bangarorin da suka hada da ruwa da tsaftar muhalli.

A cewarta, hukumar ECA ta kafa sashen kula da bangarori masu zaman kansu da hada-hadar kudi, wanda wani bangare na aikinsu shi ne, taimakawa kasashe mambobin hukumar aiwatar da hadin gwiwar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China