Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matasan Afirka sun fara rangadin kimiyya da fasaha a kasar Sin
2019-05-07 10:54:48        cri

A jiya ne wasu matasa masu bincke da jami'ai 25 daga kasashen Afirka 18 suka fara wani rangadin kimiyya da fasahar kere-kere na kwanaki 9 a kasar Sin, da nufin kara kwarewarsu a fannin kirkire-kirkire.

Yayin wannan rangadi wanda ma'aikatar kimiyya da fasahar kere-kere tare da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen kasar suka shirya, ana sa ran matasa da jami'an za su ziyarci jami'ar Tsinghua, da cibiyar nazarin aikin gona ta kasar Sin, da yankin raya fasahohin zamani dake Yichang da sauran cibiyoyin bincike da wuraren al'adu dake Beijing da lardin Hubei.

Da take karin haske kan rangadin, mataimakiyar jami'ar ayyuka ta EU dake aiki a ma'aikatar ilimi mai zurfi da cibiyar binciken kimiyya ta kasar Masar Soha Mostafa, ta ce ziyarar wata dama ce da matasan za su ziyarci daya daga abokan huldarsu. Ta ce, manufar ziyarar ita ce, kara aiwatar da nasarorin da aka cimma, yayin taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a shekarar 2018 a birnin Beijing na kasar Sin, da yayata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a fannin kimiyya da fasahar kere-kere.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China