Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hukumomin yaki da cin hanci na kasashen Afrika sun hadu a Uganda domin sake sabunta ayyukansu
2019-05-07 10:54:43        cri

Shugabannin hukumomin yaki da cin hanci na wasu kasashen Afrika, sun fara wani taron yini 6 a jiya Litinin a babban birnin Kampala na Uganda, domin musayar dabarun ayyukansu da nufin karfafa hadin gwiwa a kokarin yaki da ta'adar cin hanci.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni, da ya bude taron na 9 na shugabannin hukumomin yaki da cin hanci na kasashe renon Ingila, ya bayyana wa wakilai daga kasashe 16 muhimman batutuwa 3 dake bukatar warwarewa a yaki da cin hanci.

Ya ce, ya kamata a gudanar da binciken kwakwaf da karfafa gabatar da kara a kotu da kuma sanya kotunan yanke hukunci ba tare da bata lokaci ba.

Ya ce, za a iya nasarar yaki da cin hanci, abun da ake bukata kawai shi ne, hada hannu domin cimma wannan buri.

A cewar hukumar yaki da cin hanci ta Uganda, taron zai samar da wani dandali na musammam na musayar sabbin hanyoyi mafi dacewa na yaki da cin hanci da kuma dabarun kasa na yaki da mummunar ta'adar. (Fa'iza Msutapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China